21 Disamba 2019 - 08:15
​Rouhani: Takunkumin Amurka Kan Iran Bai Amfanar Da Ko Wata Kasa Ba

Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya ce ficewar Amirka daga cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran bai amfanar da ko wata kasa daga cikin jerin kasashen da suka cimma wannan yarjejeniya ciki kuwa harda ita kanta Amirkan

(ABNA24.com) Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya ce ficewar Amirka daga cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran bai amfanar da ko wata kasa daga cikin jerin kasashen da suka cimma wannan yarjejeniya ciki kuwa harda ita kanta Amirkan

A yayin da ya amsa goran gayyatar firai ministan kasar Japon, a jiya juma'a shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewa wajibi ne ko wata kasa ta yi aiki da kudiri mai lamba 2231 na kwamitin tsaron MDD, kuma takunkumin zalincin da kasar Amurka ta kakabawa kasar Iran ta'addanci ne na tattalin arziki, kuma duk kasashen dake yaki da ta'addanci ya kamata su yaki wannan ta'addanci.

Rouhani ya kara da cewa kasar Iran za ta yi duk wani kokari na gani ta kare yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen Duniya biyar gami da kasar Jamus wanda zai amfani kasarta kamar yadda kuma ya bukaci kasashen dake cikin wannan yarjejeniyana su mutunta ta.

Shugaba Rouhani ya ce matakin da kasar Iran ke dauka na jingine wani bangare na yarjejeniyar na zuwa ne bayan da kasashen Turai suka kasa cika alkawarin da suka dauka.

A nasa bangare firai ministan kasar Japon ya nuna farin cikinsa dangane da yadda shugaba Rouhani ya amsa gayyatar ta sa, inda ya ce kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen Iran da japon ta shiga cikin shekaru na 90, kuma kai kawon da mahukuntan kasashen biyu ke yi a tsakaninsu cikin shekarun baya-bayan nan zai kara karfafa kyakkyawar alakar dake tsakaninsu.


/129